Isa ga babban shafi
Mali

Sojojin Faransa sun kashe ‘Yan ta’adda 10 a Mali

Sojojin Faransa sun kashe mutane 10 da suka ce ‘yan ta’adda ne da ke da alaka da kungiyar Almurabitun a kusa da garin Menanka da ke cikin kasar Mali.

Mayakan Al Murabitoun sun kashe mutane da dama a harin  otel din Radisson Blue a Bamako
Mayakan Al Murabitoun sun kashe mutane da dama a harin otel din Radisson Blue a Bamako AFP/AFP/
Talla

A sanarwar da Ma’aikatan tsaron ta fitar tace an shafe sa’o’i hudu sojojin Faransa na musayar wuta da mayakan da ke da alaka da Al Qaeda.

Ma’aikatar tsaron  ta ce  mutanen na amfani ne da babura wajen kai hare-hare, kuma an same su dauke da makamai da dama.

Faransa ta zargi kungiyar Almurabitun da kai hare hare a Mali da Nijar.

A 2013 ne aka mayakan Belmokhtar da MUJAO suka kafa kungiyar Al Murabitun bayan sun hade a waje guda domin da’awar jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.