Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus za ta tura dakaru 650 zuwa Mali

Kasar Jamus za ta aika dakaru 650 zuwa Mali, a wani mataki na dadada wa Faransa dangane da yakin da ta ke yi da mayakan jihadi bayan ta fuskanci harin ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 129 a birnin Paris.

Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen  da wasu daga cikin dakarun kasar
Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen da wasu daga cikin dakarun kasar REUTERS/Wolfgang Rattay
Talla

Ministar tsaron Jamus ce, Ursula von der Leyen ta sanar da wannan matakin, a dai dai lokacin da shugabar gwamanatin kasar Angela Merkel ta isa birnin Paris na Faransa domin ganawa da shugaba Francois Hollande kan hare haren ta’addancin da kungiyar ISIS ta kai wa kasar a ranar 13 ga wannan watan na Nuwamba.

Bayan kammala taron kwamitin tsaro na majalisar dokokin Jamus, von der Leyen ta fadi cewa, dole ne su mara wa Faransa baya tare da yin duk abinda ya dace dominn tinkarar halin da Faransan ke ciki.

Ministar ta kara da cewa dakarun da za a aika kasar Mali za su mayar da hankali ne kan tattara bayanan sirri da kuma kai daukin kayayyakin soji .

A jawabin da ta gabatar a gaban majalisar dokiki a baya, shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel ta ce kasar za ta nuna goyon bayanta dari bisa dari ga Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.