Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Al Qaeda ta kai hari a wata Otel a Burkina Faso

Wasu ‘Yan bindiga sun abkwa wani ginin wata babbar Otel a Burkina Faso inda suka yi garkuwa da mutane tare da kashe wasu da dama. Rahotanni sun ce har yanzu ana barin wuta a otel din bayan jami’an tsaron Burkina Faso tare da taimakon dakarun Faransa sun farwa mayakan.

Mutane kimanin 20 aka kashe a harin da Al Qaeda ta kai a wata Otel da ke Ouagadougou
Mutane kimanin 20 aka kashe a harin da Al Qaeda ta kai a wata Otel da ke Ouagadougou REUTERS
Talla

Hukumomin Burkina faso sun ce an yi nasarar kubutar da mutane kimanin 63 a safiyar yau Assabar wadanda ‘Yan bindiga suka yi garkuwa da su a Otel din da ke Ouagadougou da mafi yawanci baki ‘yan kasashen waje ke sauka.

Tuni kungiyar Al Qaeda reshen Maghreb ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin inda aka tabbatar da mutuwar mutane sama da 20.

Cikin mutanen da kuma aka kubutar akwai 33 da suka samu raunika.

Hartin na Splendid hotel a Ouagadougou na zuwa duka kasa da wata guda da mayakan na Al Qaeda a Afrika suka kai irin harin a Radisson Blu a Bamako kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.