Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Kabore ya yaba da zanga zangar kifar da Campore

Sabon shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya yaba wa matasan da suka gudanar da zanga zangar da ta kifar da gwamnatin shugaba Blaise Compaore a shekarar da ta gabata. 

Sabon Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Lahadi
Sabon Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Lahadi AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Yayin da yake jawabi bayan karbar ranstuwa a gaban dubban al’ummar kasar, shugaban ya yi alkawarin aiwatar da sauye sauye a hukumomin gwamnati da demokiradiyar kasar da bangaren shari’a da kuma tabbatar da ‘yancin bil- Adama.

Cikin shugabanin da suka halarci bikin rantsar da Kabore har da na kasashen Benin, Gabon, Ghana, Guinea, Cote d’Ivoire, Mali, Nijar da Senegal.

Akwai dai manyan kalubale da dama da ke gaban sabon shugaban, da suka hada da makomar rusashshiyar rundunar dakaru da ke kare lafiyar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore da kuma makomar sojoji da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin rikon kwarya ta kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.