Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane sama da 50 a yini guda

Boko Haram ta kashe mutane sama da 50 jerin hare haren kunar bakin wake da ta kai a garin Gombe a arewacin Najeriya da kuma garin Marwa a arewacin Kamaru, wannan na zuwa ne a yayin da mayakan ke ikirarin samun galaba tare da barazanar sabbin hare hare a wani sakon bidiyo da suka aiko a Twitter.

Mayakan da ke addabar arewacin Najeriya
Mayakan da ke addabar arewacin Najeriya Youtube
Talla

Kimanin mutane 42 suka mutu a tagwayen hare haren da Boko Haram ta kai a  a garin Gombe arewacin Najeriya.

Mutane da dama ne kuma suka jikkata a hare haren da aka kai a tashar Dadin kowa, da unguwar Dukku a cikin garin Gombe.

A yinin Laraba ne kuma Boko Haram ta kashe mutane 11 a wani harin kunar bakin wake da wata mace ta kai a garin Marwan arewacin Kamaru

A cikin rahoton Wakilin RFI hausa Ahmed Abba ya ce mutane 13 suka mutu a harin Marwa yayin da sama da 30 ke kwance a Asibiti.

Wasu mazauna garin Marwa sun ce wata yarinya ce ‘yar kimanin shekaru 15 ta kai harin a Marwa.

"Ta zo ne tana bara sanye da hijabi" a cewar Amadu Babale mazauni unguwar Tabarmare inda aka kai harin kunar bakin waken.

Yanzu haka mahukuntan Kamaru sun tsaurara matakan tsaro a yankin Marwa bayan harin na biyu da mayakan Boko Haram suka kai a cikin wannan watan na Yuli.

A ranar 30 ga watan Yuli ne dai dakarun hadin-guiwa na kasashen Kamaru da Nijar da Najeriya da Chadi da Benin za su kaddamar da yaki domin murkushe mayakan Boko Haram.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ke ziyara a Amurka, ya nemi taimakon mahukunatan Washington akan Boko Haram musamman taimakon makamai da Amurka ta ki ba Najeriya saboda fargaba akan keta hakkin bil’adama da ta ke ganin yana taimaka wa rikicin Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.