Isa ga babban shafi
Nigeria

‘Yan Mata sun kai hare haren kunar bakin wake a Damaturu

Akalla mutane 13 suka mutu a jerin hare haren kunar bakin wake da wasu ‘Yan Mata guda uku suka kai a garin Damaturu na Jihar Yobe yayin da al’ummar Najeriya ke gudanar da bikin Sallah bayan idar da azumin watan Ramadan.

13 dead as Nigerian girls launch triple suicide bombings
13 dead as Nigerian girls launch triple suicide bombings RFI Bedu
Talla

Mazauna garin Damaturu sun ce an kai hare haren ne a kusa da harabar Masallacin Idi lokacin da al’ummar Musulmi ke shirin gudanar da Sallah.

Daya daga cikin ‘Yar Kunar bakin waken ta tayar da Bom din ne bayan Jami’an agaji sun hana ta shiga sahun Mata, kamar yadda Limamin Masallacin da aka kai harin Shiekh Babagana Malam Kyari ya shaidawa RFI Hausa.

Hukumar ‘Yan sandan Jihar Yobe ta tabbatar da mutuwar Mutane 13 a harin na Damaturu.

Damaturu babban birnin Jihar Yobe ya dade yana fama da hare haren Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.