Isa ga babban shafi
Najeriya

An sami bama bamai a majami'ar garin Jos a Najeriya

Yau Lahadi aka gano wasu bama bamai 2 a majami’ar ECWA dake Unguwar Tudun wada dake birnin Jos a arewacin Najeriya. An gano bom daya a bandaki ne, yayin da aka gano daya a wajen majami’ar. 

Wani harin da Boko Haram ta kai a Najeriya cikin hekarar bara
Wani harin da Boko Haram ta kai a Najeriya cikin hekarar bara REUTERS/Stringer
Talla

Ko dayake jami’an ‘yan sanda su kwance daya daga ciki, amma kuma daya tarwatsem amma kuma ba wanda ya sami rauni.
Harin na zuwa ne a mako guda bayan da aka kai wasu hare hare kunar bakin wake a wajen wa’azi, da wajen cin abinci a birnin na Jos, inda mutane 51 suka mutu wasu 47 suka sami raunuka.
A wani bangaren kuma, yau Asabar da sanyin safe Soja daya da ‘yan Boko Haram 3 sun mutu, lokacin da ‘yan ta’addan suka kai farmaki a wani gidan yarin dake kudancin kasar Niger.
Hukumomin gwamnati da kungiyoyin agaji sun tabbatar da aukuwar harin, da ake gani a matsayin kokarin ‘yan Boko Haram din, na ‘yantar da ‘yan uwansu dake tsare a gidan yarin.
Wata majiya tace, harin na gidan Yarin garin Diffa mai iyaka da kasar Niger, ya auku ne tsakanin karfe 1 zuwa 2 na dare agogon kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.