Amnesty ta damu da kisan mutane da Boko Haram suka yi a Baga
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty ta tabbatar da harin da mayakan kungiyar book haram suka kai a garin Baga na jihar Borno a Nigeria, inda suka kashe a kalla mutane dubu 2
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar ta ce ta sami tabbacin hakan ne ta hanyar hotunan da ta samu daga tauraron dan Adam.
Cikin sanarwar da ta fitar kungiyar ta Amnesty tace tayi binciken ta ne kan 2 daga cikin garuruwa da dama da mayan na Boko Haran suka far wa.
Hotunan da kungiyar ta Amnesty ta fitar sun nuna yadda mayakan suka yi fata fata da garin Baga da Doron Baga, inda aka ga gine gine kusan dubu 4 a lalace. Suma sauran garuruwan dake gewaye da garin basu tsira daga harin ba.
Wani mutum mai shekaru 50 da wani abu da kungiya ta ji bahasi daga gare shi, yace an kashe mutane da dama yayin harin na makon daya gabata, inda shi da sauran mutane suka tsere, mayakn suna kai musu harbi.
Wani mutumin yace mayakan na Boko Haram suna harbi kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutanen da suka hada da yara kanana.
Kungiyar ta bayyana takaicinta kan yadda jami’an tsaro basa yin abinda ya dace, don kare fararen hula daga cin zarafin da ‘yan book Haram din ke yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu