Isa ga babban shafi
UGANDA

Kotun Uganta ta haramtawa ‘Yan jarida buga hutunan ‘Yan luwadi

Wata kotu a kasar Uganda ta yanke hukuncin amincewa da wata kara da aka shigar kan haramtawa ‘yan jarida buga hutunan ‘yan luwadi, Inda Alkali mai shari’a a kotun yace buga hutunan ‘yan luwadin ya sabawa dokar ‘yancin bil’adama a tsarin dokar kasar.Wani wanda ya wakilci masu rajin kare hakkin ‘yan luwadi, yace alkalin ya yanke sahihin hukunci ne wanda zai yaki wani shafi da ake wallafawa a jaridu da ke nuna zahirin la’antar ‘yan luwadi.Wannan koken dai wasu ‘yan luwadi uku ne daga wata kungiya da ke yakin neman kare hakkin ‘yan luwadi mai suna Sexual Minorities Uganda suka gabatar a kotu, wadanda jaridar Rolling Stone ta buga hutunansu da bayanan da suka shafe su.Alkalin da ya gabatar da shari’ar Musoke Kibuuke yace wannan wata dama ce ta yin barazana ga rayuwarsu domin labarin jaridun fallasa ne.A wani bayani da jaridar Rolling Stone ta wallafa, jaridar ta zayyana jerin sunayen mutane sama da ashirin wadanda editan jaridar ya tabbatarwa al’ummar kasar ‘yan luwadi ne.  

Tutar kasar Uganda
Tutar kasar Uganda
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.