Isa ga babban shafi
Kenya

Shugaba Kibaki Ya Kaddamar Da Sabon Kundin Mulki

Kasar Kenya yau Juma'a ta  fara aiki da sabon kundin tsarin mulkin kasar, inda aka yi kasaitaccen buki daya sami halarcin Shugabannin kasashen Afrika da dama. Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir na daga cikin Shugabannin kasashe dake halartan bukin. Kasancewar yana halartan bukin yasa ‘yan kallo sun fi maida hankulansu a kansa.A wajen wannan gagarumin buki, Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki ya rattaba hannu cikin kundin tsarin mulkin inda ya zama doka da za'ayi amfani dashi a kasar.Wannan kundi ya sami amincewar da babban rinjaye, daga jamaa a zaben raba gardama da aka gudanar farkon wannan watan, da niyyar gani ba'a sake maimaita rikicin siyasar data kaiga rasa rayukan mutane 1,000 ba, lokacin zaben shekara ta 2007.Sabon kundin tsarin mulkin na maye wanda ake amfani dashi ne tun shekara ta 1963, lokacin da kasar ta sami ‘yancin kai.Daga cikin Shugabannin kasashen dake halartan bukin akwai Shugaban kasar Uganda Yoweri Musaveni da Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da Shugaban kasar Comoros Ahmed Abdallah Sambi. 

Shugaban Kenya Mwai Kibaki na maraba da Shugaban Sudanese President Omar al Bashir a wajen bukin na yau
Shugaban Kenya Mwai Kibaki na maraba da Shugaban Sudanese President Omar al Bashir a wajen bukin na yau rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.