Isa ga babban shafi
Turkiyya-Syria

Dan Sandan daya tsinto gawar yaro a Turkiyya ya bayyana halin da ya sami kansa

Dan sandan kasar Turkiyya da aka ni hotonsa yana dauko gawar yaron nan da kasar Syria dake gudun hijira tare da mahaifiyarsa da dan uwansa, yace yayi tunanin dansa, a lokacin da ya gawar yaron a gabar ruwa.

Aylan Kurdi lokacin da yake raye
Aylan Kurdi lokacin da yake raye REUTERS/Kurdi family/Handout via Reuters
Talla

Lokacin da yake magana da wata kafar yada labarun kasar ta Turkiyya, Mehmet Ciplak yace lokacin da ya tsikaye shi a kwance, sai yayi ta addu’ar fatan yaron na raye, amma yace lokacin da yaga bashi da rai yaji matukar bakin ciki.
Aylan Kurdi mai shekaru 3, da dan uwansa mai shekaru 4 Ghaleb, sun nutse ne ciki kwale kwale tare da mahaifiyarsu Rihana lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turai.
Ranar juma’a aka yi jana’izar yaron, tare da dan uwan nasa da kuma mahaifiyarsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.