Isa ga babban shafi
EU

Matsalar bakin haure na ci gaba da zafafa a nahiyar Turai

Kasashen Turai, dake fuskantar matsalar bakin haure data fi muni tun byan yakin duniya na 2, suna ci gaba da neman hanyoyin karbar mutanen dake tserewa daga Syria, dama sauran kasashen duniya.

Wasu daga cikin Bakin haure dake kokrin tsallaka wa turai
Wasu daga cikin Bakin haure dake kokrin tsallaka wa turai REUTERS/Marko Djurica TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Sai dai duk da haka kasashen na Turai sun gagara cimma matsaya kan yadda zasu bullowa lamarin.
Kokarin da ake yi na sake rarraba bakin hauren tsakanin kasashen taraiyyar Turai na samun cikas, sakamakon rashin hadin kai tsakanin Gwmnatocin yankin.
Matsalar ta baki haure ta sake ta’azzara a cikin ‘yan kwanakin nan, inda ake kara samun bakin hauren dake shiga ta kasashen yankin Balkans, suna karuwa kan wadanda ke fuskantar hadari, suna tsallaka tekun Meditereniya zuwa nahiyar Turai.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, data kai ziyara a wani sansanin da aka tsugunar da bakin haure, ta lashi takobin cewa ba za a lamunci yadda wasu ke cin zarafin bakin haure ba, duk kuwa da adawa da matakin karbar bakin haure daga masu ra’ayin mazan jiya.
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon dake ziyara a Faransa, ya nemi kasashen na Turai su nuna karamcin da aka sansu dashi, wajen kara kokari don ganin an kawo karshen matsalar.
Matsalar ta bakin haure na ci gaba da zafafa, inda yau Laraba aka tsinci gawarwakin wasu mutane 40 dake kokarin shiga Turai, cikin wani kwale kwale a gabar ruwan kasar Libya.
Yau Laraba sai da ‘yan sandan kasar Hungary suka harba hayaki mai sa kwalla, don hana wasu bakin haure kimanin 200, dake kokarin ficewa daga babbar cibiyar tantance bakin haure dake Roszke.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.