Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa zata samar da karin gidaje ga bakin haure dake shigowa

Yau Laraba hukumomin kasar Faransa sun kaddamar da wani shirin da za a samar da gidaje dubu 10,500, ga bakin haure dake shigowa kasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turai suke kokarin neman hanyoyin shawo kan matsalar bakin haure, dake tsallaka tekun Meditereniya. 

Mnistan cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve
Mnistan cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Ministan harkokin cikin gida Bernard Cazeneuve da ya bayar da sanarwar gina gidajen, yace gwamnati zata samar da gidajen ne ga wadanda azabtarwa, cin zarafi, yunkurin dauri ko kisa, suka sa su tserewa daga kasashen su.
Gwamnatin ta shirya samar da gidaje 5,000 ga mutanen da aka baiwa mafaka a Faransa, guda dubu 4,000 kuma ga masu neman mafakar, yayin da kuma za a gina gidajen 1,500 don bukatar gaggawa ga bakin haure dake shigowa ba bisa ka’ida ba.
Lokacin da yake mai da martani ga kasar Italiya dake ci gaba da kira ga sauran kasashen Turai su kara kokarin ganin sun rage mata nauyin da bakin haure ke dora mata, Ministan yace hukumomin na birnin Paris suna iya kokarinsu a wannan bangaren.
Yawan bakin haure dake shiga Faransa ya kusa ninkawa zuwa fiye da 66,000 cikin shekaru 7, yayinda hukumar dake kula da iyakokin Turai tace fiye da mutane 100,000 ne suka tsallako nahiyar a wannan shekarar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.