Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Turai

Kungiyar EU zata duba matsalar kwararar bakin haure a nahiyar Turai

Shugaban Hukumar kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk na duba yuwuwar kiran taron gaggawa gameda batun bakin haure sakamakon mummunar hasarar rayukan bakin haure da aka samu na baya bayan nan inda rayukan bakin haure akalla 700 suka salwanta a tekun meditareniya. Mutanen sun mutu ne lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa ci rani a Nahiyar Turai.Bayanai na cewa MR. Tusk yana duba kiran taron cikin gaggawa ne, domin duba yadda za a kawo karshen wannan matsalar.Shugaban Faransa Francois Hollande yace idan har ta tabbata cewa mutanen sun bace a teku ne, to wannan ne zai kasance hasarar rayukan bakin haure mafi muni a tarihi.Bakin haure suna yawan rasa ransu a kokarin da suke yi, na tsallakawa zuwa nahiyar Turai, daga Africa. 

Shugaban hukumar taraiyyar Turai ta EU, Donald Tusk
Shugaban hukumar taraiyyar Turai ta EU, Donald Tusk REUTERS/Francois Lenoir
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.