Isa ga babban shafi
Faransa-Ja,us

Kasashen Faransa da Jamus suna duba matsalar bakin haure tsakaninsu

Yau litinin shugabannin Kasashen Jamus da Faransa zasu gana a birnin Berlin, domin samar da matakan bai daya, na magance matsalar kwararar bakin haure dake ci gaba da tsallakawa nahiyar Turai.

Shugaban Faransa, Francois Hollande tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugaban Faransa, Francois Hollande tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Reuters/路透社
Talla

An dai danganta matsalar kwarara bakin haure na wannan karan a matsayin mafi kamari tun bayan yakin duniya na biyu, yayin da kuma sama da bakin haure dubu biyu suka kutsa kai cikin kasar Serbia, daga Mercedonia a daren jiya kadai, da nufin samun ingantacciyar rayuwa.
Wannan kuma na zuwa ne bayan Mercedonia ta janye dokar ta baci, data sanya akan iyakaryta da Girka saboda matsalar kwararar bakin hauren.
Gabanin tattaunawar shugabannin 2, Shugabar gwamantin Jamus, Angela Merkel ta yi Allah wadai da zanga zangar adawa da bakin haure da yan kasar ta ke yi tare da kyamatarsu.
A bangare guda kuma, ministan harkokin wajen kasar Austria, Sebastian Kurz ya bayyana matsalar kwarrar balkin haure a matsayin matsalar tabarbarewar halin rayuwa, inda kuma ya bukaci a samar da sabbin tsare tsaren dakile kwararar bakin.
Hukumar dake kula da kan iyakokin kasashen Turai ta bayyana cewa kimaninn bakin haure 340,000 ne suka shiga nahiyar Turai cikin watanni bakwai na farkon wannnan shekarar.
Akasarin yan ciranin na kwauracewa yake yake ne da talauci harma da kuncin rayuwa, abinda ya sa suke barin kasashen su na asali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.