Kasashen Austria da Jamus sun fara karbar bakin haure daga Hungary
Yau Asabar da sanyi safe motocin farko dake dauke da bakin haure, sun tashi daga kasar Hungary zuwa Austria, bayan da mahukunta biranen Vienna da Berlin sun amince su karbi dubun dubatar bakin dake yashe a Budapest.
Wallafawa ranar:
Wani wakilin kamfanin dillacin labarun Faransa na AFP dake wajen yace, mota daya kirar Bus, ta tashi daga filin jirgin kasa na Keleti, inda baki masu yawa ke jiran a kaisu yammacin nahiyar Tura.
An kuma ga wasu motocin na dibar wasu bakin kimanin 1,200, da suka fara tattaki, suka nufi kan iyakar kasar ta Hungary.
Lamarin bakin haure ya dauki hankulan duniya cikin wannan makon, bayanda wani kwale kwale ya kife a kan tekun kasar Turkiyya, inda mutane suka mutu, ciki har da wani yaro mai shekaru 3 a duniya, dan kasar Syria, da suka tsere tare da mahaifiyarsa da dan uwansa.
Wannan lamarin ya tayar da hankulan al’ummomin duniya da dama, inda wasu ke ganin ya kamata a sake duba matsalar ta bakin haure.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu