Isa ga babban shafi
Austriya-Bakin Haure

An gurfanar da mutane 4 a gaban kotu ana zarginsu da hannu a mutuwar bakin haure 71

Mutane 4 ne aka kama da kuma ake zargi da hannu a cikin haddasa mummunan al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar bakin haure 71 da aka gano gawawwakinsu a watan motar kontina, da aka faka a gefen hanya a kasar Ostria, inda a yau assabar aka gurfanar dasu a gaban wata kotun kasar Hongri , kwanaki 2 bayan faruwar mummunan al’amarin. 

yan sandan kasar Ostria da na Hongri na bincike kan hadarin da yayi sanadiyar mutuwar bakin hauren
yan sandan kasar Ostria da na Hongri na bincike kan hadarin da yayi sanadiyar mutuwar bakin hauren REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

Ana  zargin mutanen ne, da zama mambobin wata kungiyar yan tsageran kasashen Bulgeriya da Hongri , dake safarar yan Adam a nahiyar ta Turai.

Gawwakin mutane 71 dayan da aka gano a cikin motar daukar kayyan marmari, da suka hada da yara 4 yan kasar Syriya ne, da ke tserewa yakin da ake tafkawa a kasarsu, zuwa nahiyar Turai, neman rayuwa mai sauki.

Yanzu haka dai masana kiyon lafiya na ci gaba da gudanar da binciken gano yadda aka yi wadannan mutane suka rasa rayukansu, al’amarin da ya kara tada hankalin mahukumtan nahiyar Turai da na Majalisar Dinkin Duniya, ganin irin munin da kwararar bakin haure a turai ke dada haddasawa a  halin yanzu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.