Isa ga babban shafi
Balkans

Kasashen Yankin Balkans na taro kan bakin haure

Shugabannin kasashen yankin Balkans na gudanar da wani taro a birnin Vienna inda suke duba matsalar bakin haure da kuma yadda za a magance ta a nahiyar turai.  

Dubban Baki ne suka tsallaka nahiyar Turai cikin wannan shekarar
Dubban Baki ne suka tsallaka nahiyar Turai cikin wannan shekarar REUTERS/Ognen Teofilovski
Talla

Wannan na zuwa ne bayan an gano gawarwakin bakin haure 50 a wani sunduki da ya tsaya a kasar Austria, al-amarin da ya zama wani babban gargadi ga shuagabannin nahiyar ta Turai dake bukatar magance matsalar.

Daga watan Janairu zuwa Yunin wannan shekarar kimanin bakin haure dubu 102 ne suka bi ta sabuwar hanyar da ake kira hanyar Balkans domin samun damar kutsa kai a nahiyar Turai

Kwararar bakin hauren dai ta karu ainun ta wannan hanyar, idan aka auna da shekara ta 2014 inda bakin haure dubu 80 suka bi ta kasashen Balkans a dai dai irin wannan lokacin.

Ita dai hanyar da ta taso daga kasar Turkiya zuwa kasar Girka, tana zarcewa ne ta rasta kasashen Macedonia da Serbia.

Sannu a hankali dai bakin hauren da galibi yan gudun hijira ne na ci gaba da baiwa wannan hanya muhimmanci, a daidai wannan lokacin da ake fuskantar hasarar rayukan bakin hauren dake bi ta gabar tekun Libya, domin shiga Turai kamar yadda hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a ta sanar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.