Isa ga babban shafi
Isra'ila

An sako ‘yan ci-rani Afrika da aka tsare a kurkukun Isra’ila

Kasar Isra’ila ta sako wasu daruruwan baki haure ‘yan Afrika, da ake tsare da su a wani kurkukun ihunka banza bisa umarni wata kotun kasar.Sai dai kuma an haramtawa masu neman mafakar siyasa acikin bakin, shiga wasu biranen kasar 2.

REUTERS/Amir Cohen
Talla

Kotun kolin kasar ta baiwa mahukuntan kasar ta Isra’ila umarnin sakin mutanen su kusan 1,200, da ake tsare da su yau kusan shekara guda a kurkukun ihunka banza da ke Nagev.

Wani mai magana da yawun gidan kurkukun ya ce, yau Talata aka sako 750 daga cikin mutanen, yayin da kuma ake sa ran sako sauran gobe Laraba.

An ga mutanen, da ke ficewa daga kurkukun suna neman motacin da za su taimaka musu barin yankin, inda kuma suke gararambar neman inda za su tsuguna, bayan da aka haramta musu zama a biranen Tel Aviv da Eilat, inda dama aka samu tumbatsar bakin haure ‘yan Afrika.

Kamar sauran sassan duniya, matsalar kwararar bakin haure na ci gaba da zama babbar matsala a kasar Isra’ila, inda ‘yan siyasa daga bangaren ‘yan mazan jiya ke kiran a dauki matakan takaita shigar bakin, yayin da ‘yan rajin kare hakkin dan Adam ke neman gwamnati ta kyale baki, musamman daga kasashe irinsu Eritrea.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.