Isa ga babban shafi
Nijar

An sassauta dokar hana babura a Nijar

Mahukuntan jiahar Diffa da ke kudancin Jamhuriyar Nijar, sun sassauta haramcin hana amfanin da babura a jihar, in da suka bada umarnin yin amfani da babur mai kafa uku, da aka fi sani da a daidaita sahu, domin ragewa jama’a wahalhalu a birnin.

Hukumomin Diffa da ke Nijar sun amince a yi amfani da a daidaita sahu  don zirga-zirga a maimakon babura a jihar
Hukumomin Diffa da ke Nijar sun amince a yi amfani da a daidaita sahu don zirga-zirga a maimakon babura a jihar
Talla

Jihar Diffa da ke fama da rikicin Boko Haram, ta haramta amfani da Babur tare da takaita zirga-zirgar ababen hawa a karkashin dokar ta baci da gwamnati ta kafa a jihar, domin samun damar inganta tsaron rayuka da kuma dukiyoyin a’umma.

A hirarsa da RFI hausa, gwamnan jihar ta Diffa, Malam Lawali Dandano ya ce, duk mai bukatar amfani da babur mai kafa uku, na iya gabatar da kansa don samun izinin hukumomi don aiki da shi a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa, an fara samun kwanciyar hankali a jihar saboda yadda 'yan bindiga ke tuba tare da mika wuya ga hukumomi.

Gwamnan ya ce, ko a wannan Laraba sai da wasu daga cikin mayakan Boko Haram  suka mika kansu, yayin da ya y kira ga sauran mayakan da su yi koyi da wadanda suka tuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.