Isa ga babban shafi
GASAR TURAI

Mun shirya yiwa kungiyar Arsenal illa a karawar yau - Tuchel

Turai – Mai horar da 'yan wasan kungiyar Bayern Munich, Thomas Tuchel ya gargadi Arsenal cewar a shirye suke su mata rauni a karawar da za suyi yau na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Bukayo Saka (Arsenal) après avoir marqué un but contre Lens, en Ligue des Champions, à Londres, le 29 novembre 2023.
Bukayo Saka (Arsenal) après avoir marqué un but contre Lens, en Ligue des Champions, à Londres, le 29 novembre 2023. © Kin Cheung/AP
Talla

Tuchel ya bayyana Arsenal a matsayin kungiyar da ta fi kowacce a gasar Firimiya kamar yadda alkaluman gasar suka nuna, wanda ya ce ya dace da kungiyar saboda kasancewar ta a matsayi na farko a teburin Firimiya.

Manajan yace kungiyar na da karsashi sosai kuma hakan ya nuna a wasannin ta na shekaru 2 da suka gabata, saboda haka yace karawar su ta yau za ta zama zakaran gwajin dafi a gare su, saboda wasu 'yan matsalolin da suke fuskanta a 'yan kwanakin nan.

Yan wasan Arsenal na murnar nasarar da suka samu
Yan wasan Arsenal na murnar nasarar da suka samu © AFP - GLYN KIRK

Tuchel yace wannan itace shekara ta 2 da Arsenal ke nuna matukar kwazo, kuma 'yan wasan ta na da karsashi sosai ganin cewar akasarin su matasa ne masu kananan shekaru.

Manajan yace su ma sun san irin karfin da kungiyar su ta Bayern Munich ke da shi da kuma irin illar da suke so su yiwa abokan karawar su, saboda irin kwarewar da suke da shi a wannan gasa ta cin kofin zakarun Turai wanda suka yi fice a cikin sa.

Wannan shine karo na farko da Arsenal ke shiga gasar cin kofin zakarun Turai bayan shekaru 14, kuma karawar ta yau na da matukar tasiri a gare ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.