Isa ga babban shafi

Mbappe ya sha alwashin nuna bajintarsa a wasan PSG da Barcelona

Kylian Mbappe ya ce zai yi fice a wasan da ƙungiyarsa PSG za ta fafata da Barcelona a matakin daf da kusa da ƙarshe a gasar zakarun nahiyar Turai a wannan makon.

Kylian Mbappé c
Kylian Mbappé c AFP - MIGUEL MEDINA
Talla

Mbappé,  mai shekaru 25 ya lashe kofuna 13 daa ƙungiyarsa ta ƙasar Faransa, PSG, ciki har da kofin ligue guda 5, amma har yanzu bai kai ga cin kofin zakarun Turai da wannan kungiyar ba.

Tun  da farko rahotanni  sun bayyana cewa ana sa ran zai koma Real Madrid  a ƙarshen wannan kaka, lokacin da kwantiraginsa da PSG zai ƙare, kuma  hakan nufin cewa wannan zai kasance yunƙurinsa na ƙarshe na lashe kofin zakarun Turai da ƙungiyar ta ƙasar Faransa.

A ganawar da ya yi da manema labarai gabanin wasan na su na Laraba, Mbappe ya ce ba zai bari kansa ya kulle ba, zai yi bajinta a wasan da za fafata a Parc des Princes na nan birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.