Isa ga babban shafi

Halin da ake ciki dangane da kalubalen da ke tunkarar gasar Olympics ta Paris

Kasa da kwanaki 100 da suka rage birnin Paris zai karbi bakuncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics, karon farko cikin shekaru 100 ke nan da birnin zai karbi bakuncin wannan babbar gasa. Abin tambaya a nan dai shi ne ko birnin na Paris ya kammala Shirin karbar bakuncin wannan gasa kamar yadda aka alkawuranta?

Dagin gasar Olympic da birnin Paris zai karbi bakunci.
Dagin gasar Olympic da birnin Paris zai karbi bakunci. AP - Michel Euler
Talla

Jim kadan bayan sanar da cewar birnin Paris zai karbi bakuncin gasar Olympics ta wannan shekarar a shekarar 2017, magajiyar birnin Paris Anne Hidalgo ta ce gasar za ta kayatar matuka.

Me ya banbanta gasar Olympics ta Paris?

A kokarin kawo sauyi bisa al’adar gasar, ana gudanar da bikin bude ta ne a cikin filin wasannin da aka tanada, sai dai a wannan karon masu shirya gasar ta Paris na kokarin ganin an gudanar da bikin a bakin kogin Seine, inda za a yi tafiyar kilo mita 6 a cikin kwale-kwale cikin ruwan ana gudanar da shagulgula.

Kogin Sein da za a gudanar da bikin bude gasar Olympics.
Kogin Sein da za a gudanar da bikin bude gasar Olympics. © AFP - Handout Florian Hulleu

Sai dai harin ta’addancin da kungiyar IS ta kai birnin Moscow na Rasha a ranar 22 ga watan Maris, ya sanya shakku game da gudanar da bikin, saboda tsoron barazanar kai hari a lokacin.

A tsakiyar watan Afrelun nan ne dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar, idan har aka ci gaba da samun barazanar kai hari a wajen bikin, da yuwuwar a sauya wajen bikin.

A wani sakon Email da Kwamitin Shirya Gasar ya aikewa kafar talabijin ta France24, ya ce har yanzu ba a sauya wajen gudanar da bikin bude gasar ba daga Seine zuwa Trocadero ko kuma babban filin wasa na Stade de France.

Ko za a yi wa Hasumiyar Eiffel fenti kalar zinari?

Wannan ba ya cikin bangarorin da aka yi alkawari akansa, inda ake ganin ba lalle ne a kammala aikin yi wa Hasumiyar Eiffel kwas-kwarima ba gabanin wasannin.

Aikin fenti Hasumiyar ta Eiffel da ke da tsayin mita 330, an faro shi  ne a shekarar 2019, kuma ya kamata a kammala shi ba kawai don gasar Olympics ba,  har ma da bikin cika shekaru 100 na mutuwar wanda ya tsara wannan Hasumiya ta Eiffel, Gustave Eiffel.

Hasumiyar Eiffel, da ke birnin Paris.
Hasumiyar Eiffel, da ke birnin Paris. © AFP -Stefano Rellandini

Manyan daga cikin dalilan da suka sanya aka samu jinkiri wajen kammala aiki, akwai bullar cutar Covid-19, wacce ta sa aka samu tsaiko na tsawon watanni tara da faro aikin.

Izuwa lokacin rubuta wannan rahoton da France24 ta yi, ba a tsammanin za a kammala aikin Hasumiyar Eiffel, inda ake ganin zai iya kai wa shekarar 2025 ko 2026.

Wane tanadi aka yi wa tsarin sifurin Paris a lokacin Olympics?

Bayan sayar da tikiti miliyan 8 da dubu dari 8, ga bakin da za su halarci gasar Olympics da za a yi a tsakanin ranakun 26 ga watan Yuli zuwa 11 ga watan Agusta da kuma gasar Paralympics ta masu bukata ta musamman da za gudanar a tsakanin 28 ga Agusta zuwa 8 ga Satumba duk a birnin Paris, hankali ya koma ne kan tsarin sifurin da za a yi amfani da shi a birni, inda a yanzu ake amfani da layin dogo na Metro wanda a kowce rana ake jigilar akalla fasinjoji dubu 150, sai dai adalin a lokacin gasar zai iya kai dubu dari 8 a kowace rana.

Domin saukaka tsarin sifuri, gwamnatin Faransa ta na nan tana aikin gina sabbin layukan dogo.
Domin saukaka tsarin sifuri, gwamnatin Faransa ta na nan tana aikin gina sabbin layukan dogo. © AFP - Philippe Lopez

Kawo yanzu dai akwai karin layukan dogo da ake kan aikinsu, wasu daga cikinsu ana fatan kammalawa a watan Yuni mai zuwa gabanin fara gasar ke nan.

A farkon wannan shekarar ce gwamnatin Faransa ta kaddamar da wani gangami inda ta ke bukatar mazauna birnin Paris su fara rungumar wasu tsarin sifuri kamar babura da tafiyar kafa, don kaucewa cunkoso a lokacin gasar.

Ina aka kwana a aikin wurin gudanar da gasar?

Magajin garin garin birnin Paris Emmanuel Gregoire, ya tabbatar da cewar an kammala ayyukan dukkanin wuraren gudanar da wasannin gasar Olympics da birnin zai karbi bakunci, kuma tuni na mikasu ga kwamitin shirya gasar.

Ginin wajen da za a gudanar da wasannin Olympics a birnin Paris.
Ginin wajen da za a gudanar da wasannin Olympics a birnin Paris. © AFP - Ludovic Marin

A ranar 8 ga watan Mayu, ake saran wutar wasannin Olympics za ta isa birnin Marseille na kudancin Faransa sannan ta wuce wasu kauyuka da garuruwa da birane kusan 400 kafin isa birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.