Isa ga babban shafi

Mun kammala dukkanin shirye-shiryen gasar Olympics - Kwamitin shirye gasar

Shugabannin shirya wasannin gasar Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci, sun bayyana cewar sun kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata, sannan a shirye suke don tunkarar duk wani kalubale da ka iya bijirowa gabanin fara gasar a ranar 26 ga Yuli mai zuwa.

Ofishin shirya gasar Olympic da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Juli mai zuwa.
Ofishin shirya gasar Olympic da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Juli mai zuwa. © AFP / JOEL SAGET
Talla

A lokacin da shugaban shirya gasar Tony Estanguet ke gabatar da jawabi a Auberviliers, ya yaba da yadda tun bayan baiwa birnin Paris damar daukar nauyin gasar a watan Satumbar shekarar 2017, jami’an da ke aikin shirya gasar ke aiki tukuru don ganin an cimma burin da ake son cimmawa.

Muna da tabbacin cewa tawagarmu ta shirya gasar Olympics a Paris sun dauki dukkan matakan da suka dace, mun samu nasarar kammala ayyukanmu daya bayan daya, ta fuskar gina wuraren wasanni da kudaden shiga da kuma batun tikiti.

Fargabar da ake da ita game da gasar

Tun bayan kai harin ta’addanci da kungiyar IS ta yi a birnin Moscow na Rasha a watan da ya gabata, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 144, Firaministan Faransa Gabriel Attal ya sanar da cewar kasar za ta kasance cikin shirin kota kwana.

Haka nan a ranar Talatar da ta gabata, ministan kula da harkokin cikin gidan kasar Gerald Darmanin ya bayyana fargabansa game da kai hari birnin Paris nan kusa.

Ya ce hukumomin tsaro sun kara tsaurara matakai a birnin, ganin yadda kimanin mutane dubu 50 za su kalli wasan da aka yi tsakanin PSG da Barcelona.

Wannan mataki dai ya biyo bayan bullar wani bidiyo na kungiyar IS, da ke barazanar kai hari a filayen wasan da aka buga wasannin gasar zakarun Turai a Paris da London da kuma Madrid.

Matakan kariya

Sai dai shugaban shirya gasar Olympics Tony Estanguet, ya ce tun bayan fara aikin shirya gasar sun tsammaci samun barazanar tsaro.

Shugaban kwamitin shirya gasar Olympics na birnin Paris Tony Estanguet.
Shugaban kwamitin shirya gasar Olympics na birnin Paris Tony Estanguet. AP - Christophe Ena

Ya ce sun nemi damar daukar nauyin gasar ce bayan harin ta’addancin da aka kai birnin a shekarar 2015, don haka sun dauki tsauraran matakan tsaro kan lamarin.

Estanguet ya ce babu wani lokaci a baya da Faransa ta taba daukar matakan tsaro kamar wannan, kuma yana da tabbacin cewar jami’an tsaron kasar za su samar da tsaron da ake bukata a lokacin gasar.

Tabbacin na Estanguet na zuwa ne ‘yan sa’oi gabanin kwamitin manyan ‘yan siyasar Faransa da ke majalisar dattawar kasar, za su gabatar da rahoton bincikensu na tsawon shekara guda, wanda ya duba ko kasar na da tsaron da za ta iya daukar nauyin babbar gasa ta kasa da kasa.

Waiwaye

An fara diga ayar tambaye ne gama da ko birnin zai iya daukar nauyin babbar gasa, bayan abinda ya faru a filin wasa na Stade de France, lokacin wasan karshe na gasar zakarun Turai tsakanin iverpool da Real Madrid a shekarar 2022, inda gungun wasu ‘yan ta'adda suka farmaki magoya bayan kungiyar Liverpool.

Filin wasa na Stade de France, lokacin wasan karshe tsakanin kungiyoyin Real Madrid da Liverpool a shekarar 2022.
Filin wasa na Stade de France, lokacin wasan karshe tsakanin kungiyoyin Real Madrid da Liverpool a shekarar 2022. AFP - MARYAM EL HAMOUCHI

Gabanin gabatar da rahoton asalin abinda ya faru, da dama daga cikin ‘yan siyasar Faransa ciki harda ministocin cikin gida da na wasanni, sun dora alhakin lamarin kan yadda wasu magoya bayan kungiyar suka yi kokarin kutsa kai cikin filin wasa ba tare da tikiti ba, sai dai daga bisani binciken majalisar dattawar kasar ya wanke magoya bayan tare da bayyana gaskiyar abinda ya faru.

Shugaban shirya gasar Olympics ta Paris Tony Estanguet, ya ce mutane su kwantar da hankalinsu domin hatta wajen da aka shirya don gudanar da bikin bude gasar baya fuskantar wata barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.