Isa ga babban shafi

Gasar Olympics ba ta fuskantar kowacce barazana a yanzu - Ministar Wasanni

Ministar Wasannin Faransa Amelie Oudea-Castera, ta ce a yanzu babu wata barazanar hare-haren ta’addanci da gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics da za a gudanar a birnin Paris ke fuskanta, lamarin da ya bai wa masu shirya gasar damar ci gaba da shirya yadda bikin bude gasar zai gudana a kogin Seine.

Kogin Seine na kasar Faransa, da za a gudanar da bikin bude gasar Olympics.
Kogin Seine na kasar Faransa, da za a gudanar da bikin bude gasar Olympics. AFP - FLORIAN HULLEU
Talla

Da ma dai harin ta’adancin da aka kai birnin Moscow da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 140 ne, ya haifar da barazanar game da gasar ta Olympics da za a fara a ranar 26 ga watan Yuli mai zuwa.

To sai dai uwargida Amelie Oudea-Castera, ta shaida wa kafar talabijin ta France 2 cewar, za a gudanar da bikin bude gasar kamar yadda aka tsara a Seine, duk da cewa ta ce a gafe guda suna da wani zabi na daban.

Bikin bude gasar Olympics a Kogin Seine

Tun da farko an tsara gudanar da bikin bude gasar ne a kogin Seine, maimakon cikin filin wasan da za a gudanar da gasar, inda aka shirya cewa tawagogin ‘yan wasan za su shiga kwale-kwale a kogin, da 'yan kallo kusan dubu dari 5 ciki har da mutanen da ke da gidaje kusa da wurin za su kalli bikin bude wasannin gasar.

Kogin Seine da 'yan wasa ke ninkaya a cikinsa a bikin bude gasar Olympics ta birnin Paris
Kogin Seine da 'yan wasa ke ninkaya a cikinsa a bikin bude gasar Olympics ta birnin Paris AP - Michel Euler

Dukkanin kasashen da za su halarci gasar ciki harda Amurka da Isra’ila, sun amince da shiga wasannin bude gasar da za a yi a cikin kogin.

 

A baya dai masu shirya gasar ta Olympics sun yanke hukuncin sauya tsarin yadda za a gudanar da bikin bude gasar a Seine, sai dai kuma daga bisani sun amince cewa za a takaita yadda bikin zai gudana, ta yadda 'yan wasa ne kawai za su yi amfani da kwale-kwale wajen gudanar da bikin.

Ministar Wasannin ta Faransa ta ce za a gudanar da atisayen bikin bude gasar a kogin na Seine, a ranar 27 ga watan Mayu da kuma 17 ga watan Yuni masu zuwa.

An sha kai hari a lokacin wasannin Olympics, wanda ya fi kamari shi ne na shekarar 1972 da aka yi a Munich da kuma a shekarar 1996 a Atlanta.

A kokarin tabbatar da tsaro a lokacin gasar, ma’aikatar kula da harkokin cikin gidan Faransa ta ce, a yanzu dai hukumomin tsaron kasar na aikin tantance mutane miliyan daya gabanin gasar, cikinsu kuwa har da wadanda ke zaune kusa da gine-ginen da aka tanada don gudanar da gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.