Isa ga babban shafi

Mutane dubu 14 ne ake sa ran zasu halarci gasar Olympics ta Faransa

Mashirya gasar guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympics da za’a yi a birnin Paris sun sanar da karbar makullin wajen da za’a gudanar da wannan gasa da aka yiwa lakabi da Athletes Village, a hukumance a ci gaba da shirye-shiryen da kasar ke yi na karbar bakuncin gasar.

Tambarin gasar Olympics
Tambarin gasar Olympics AP - Michel Euler
Talla

Tuni shirye-shirye sun yin isa, inda aka gama tsara manyan bakin da zasu halarci bude gasar a cikin Faransa da suka hadar da shugaban kasar Emmanuel Macron da Jagoran shirya gasar Tony Estanguet da manyan jiga-jigan tsaffin yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na faransar.

Ana sa ran kasar zata karbi bakuncin mutanen dubu 14 daga sassan duniya a gasar da zata fara ranar 26 ga watan Yuli mai zuwa, yayin da ‘yan wasa dubu 9 zasu halarta.

Tuni aka fara kai duk wasu kayayyakin da za’a yi amfani da su a wajen, kama daga kayan da ‘yan wasa zasu bukata da injina da sauran abubuwan bukatar ‘yan kallo da manyan baki.

Masu sanya idanu kan yadda shirye-shiryen karbar gasar ya gudana sun yabawa Faransa kan yadda ta shirya akan lokaci, duk kuwa da matsaloli na cikin gida da take fama da su.

Sai dai kuma tashin farashin kayan masarufi da gurguntar tattalin arziki ta tilastawa kasar kara kaso uku cikin dari na adadin kudaden da aka shirya kashewa a yayin gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.