Isa ga babban shafi

Kallo ya koma ga Harry Kane gabanin haduwar Arsenal da Bayern Munich

Dai dai lokacin da Bayern Munich ke shirin tattaki zuwa arewacin London don tunkarar Arsenal, kowa sanya idanun da ya ke shi ne ganin ko Harry Kane da ya saba ragargazar Arsenal zai ci gaba da wannan bajinta kan tawagar ta Mikel Arteta ko akasin haka.

Harry Kane, dan wasan gaba na Ingila da Bayern Munich.
Harry Kane, dan wasan gaba na Ingila da Bayern Munich. REUTERS - WOLFGANG RATTAY
Talla

Gabanin komawarsa Bayern Munich daga Tottenham, Harry Kane dan Ingila ya kasance dan wasa mafi zura kwallo a ragar Arsenal karkashin gasar Firimiya da jumullar kwallaye 14 ciki har da 5 da ya zura a filin wasa na Emirates, sai dai tambayar shi ne ko dan wasan zai iya shafe fatan tawagar Arteta na kai labari a gasar ta zakarun Turai?

Bayan komawarsa Bayern Munich, Kane ya kafa tarihi zura kwallaye 38 a wasanni 37, yanzu haka shi ke rike da kambun dan wasa mafi zura kwallo a Bundesliga bayan lashe takalmin zinare a kakar da ta gabata, kuma yanzu haka ya na da jumullar kwallaye 32.

Sai dai a bangaren Arsenal tuni kyaftin din tawagar Martin Odegaard  ya bayyana cewa ko kadan bai kamata ‘yan wasan na Arsenal su yi shakkar haduwa da Kane ba, duk da cewa sun san zarrar da ya ke da ita, amma abu mafi muhimmanci shi ne su shirya kansu.

To duk dai da wannan bajinta da Kane, kungiyarsa Bayern Munich na shirin rasa kambun Bundesliga a bana, wanda kungiyar ta yi fatan lashewa karo na 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.