Isa ga babban shafi

Real Madrid za ta doka wasan yau da nufin daukar fansa kan City- Guardiola

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola, ya bayyana cewa ko shakka babu Real Madrid za ta shiga fili a yau ne da zummar daukar fansar abin da City ta yi mata a bara.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola. AFP/File
Talla

A kakar da ta gabata, a matakin wasannin gab da na karshe na wannan gasa ne City ta lallasa Madrid da kwallaye 5 da 1 a jumulla, wanda ya kange jagorar ta La Liga mai tarihin lashe kofin na zakarun Turai har sau 14 iya kaiwa wasan karshe na baran, yayinda tawagar Guardiola ta lashe kofin karon farko a tarihi.

A cewar Guadiola ko shakka haduwar ta yau baza ta zo wa City da sauki ba, domin kuwa iya lallasa Real Madrid a jere ba abu ne mai sauki ba, yana mai cewa akwai tabbacin Madrid ta kammala gano kuskuren da ya kai ta ga shan kaye hannunsu a kakar da ta gabata, don haka a yanzu za ta shiga fili da dukkan karfinta.

Guardiola da ke matsayin tsuntsu mai wayo, wanda ya saba da salon kambama bangaren adawa gabanin haduwa, masana na ganin zai yi kokarin yin canjaras ta kowanne hali da Madrid gabanin haduwarsu ta gaba a Etihad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.