Isa ga babban shafi

Manchester City da Real Madrid sun sake gamuwa a gasar zakarun Turai

Manchester City mai rike da kambi za ta hadu da Real Madrid a matakin wasan gab da na kusan karshe a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai bayan an hada su a  jadawalin gasar da aka fitar a wannan Juma'ar.

Jadawalin Gasar Cin Kofin Zakarun Turai a matakin wasan gab da na kusan karshe.
Jadawalin Gasar Cin Kofin Zakarun Turai a matakin wasan gab da na kusan karshe. REUTERS - Denis Balibouse
Talla

Wannan na nuni da cewa, a karo na uku ke nan a kakannin wasanni da Manchester City za ta hadu da Real Madrid a Gaar ta Zakarun Turai.

Arsenal za ta fafata da Bayern Munich, yayin da Paris Saint-Germaine za ta kara da Barcelona, sai kuma Atletico Madrid wadda za ta kece raini da Borussia Dortmund duk dai a matakin wasan na kwata-fainal.

A ranar 6 ko 7 ga watan Afrilu ne Manchester City za ta yi balaguro zuwa babban birnin Spain domin wasanta da Real Madrid zagayen farko, kafin Madrid din ta kawo mata ziyara bayan mako guda da wasansu na farkon.

Manchester City ta doke Real Madrid a wasan gab da na karshe a kakar wasannin da ta gabata bayan sun buga canjaras 1-1 a Santiago Bernabeu, kafin su tashi 4-0 a gidan City a zagayr na biyu na wasan a wancan lokaci.

Za dai a buga wasan karshe na Gasar ta Cin Kofin Zakarun Turai a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa a filin wasa na Wembley.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.