Tawagar matan Najeriya sun kai matakin daf da kusa da karshe a gasar Afirka
A ci gaba da gasar kwallon kafar mata ta Afrika da ke gudana a kasar Morocco, Najeriya da Botswana sun bi sahun Afrika ta Kudu, bayan da suka kai matakin wasan daf da kusa da karshe, wato quarter finals.
Wallafawa ranar:
Banyana Banyana na Afrika ta Kudu sun doke Botswana da ci daya mai ban haushi a Rabat, lamarin da ya kai su matsayi na 1 a rukunin C, a yayin da Super Falcons na Najeriya suka lallasa matan Burundi da ci 4-0 don samun matsayi na 2.
‘Yan matan na Najeriya sun hana Burundi sakat, kuma sun nuna suna iya kara wasu kwallayen a tsanake.
Super Falcons na Najeriya za su fafata da matan Kamaru a wasan daf da na kusa da karshe a birnin Casablanca, ranar Alhamis.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu