Isa ga babban shafi
Najeriya - Wasanni

NFF zata karrama tsoffin 'yan wasan Super Falcons na1999

A wannan Litinin 20 ga watan Satumba Hukumar Kwallon kafar Najeriya NFF zata karrama tsoffin tawagar ‘yan matan Super Falcons ajin shekarar 1999 wadanda suka kai wasan daf da na kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya na mata a Amurka.

Tawagar 'yan wasan Super Falcon ta Najeriya
Tawagar 'yan wasan Super Falcon ta Najeriya NGSuper_Falcons/Twitter
Talla

Tawagar wanda kaftin Florence Omagbemi ke jagoranta, ta doke Koriya ta Arewa da ci 2-1 a filin Rose Bowl na Pasadena, Mercy Akide da Rita Nwadike, suka zuru kwallayen a wancan lokaci, kafin ta sha kashi a hannun Amurka da ci 7-1.

A yayin wannan kasaitacen buki a Hotel Eko dake birnin Lagos za’a karrama mambobi tawagar mata ta shekarar 1999 su goma sha biyar da kuma koci Ismaila Mabo, inda Takwas daga cikinsu suka taso daga kasar Amurka, sai dai abin takaici, daya daga cikin ‘yan wasan tsakiya na tawagar dake yawan kai hari, Ifeanyi Chiejine ta mutu a bara.

A bukin karrama ‘yan wasan Najeriya karo na farko da ya gudana a shekarar 2018 an samu bakwancin Shugaban FIFA Gianni Infantino sannan Shugaban CAF a lokacin Ahmad Ahmad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.