Isa ga babban shafi

Falcons ta fuskantar koma baya saboda rashin Oshoala a gasar AWCON

Yayin da tawagar ‘yan matan Najeriya Falcons ke shirin Fuskantar Botswana a wasan da Dole sai ta samu Nasara muddun tana bukatan a ci gaba da dama da ita a gasar ta Morocco, sai ga shi shaharerriyar ‘yar wasan ta Asisat Oshoala ta fice daga gasar

'Yar wasan tawagar mata ta Najariya Asisat Oshoala.
'Yar wasan tawagar mata ta Najariya Asisat Oshoala. Icon Sportswire via Getty Images - Icon Sportswire
Talla

Hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta sanar cewa 'yar wasan ta Super Falcons, Oshoala dake taka leda a Barcelona ba za ta samu damar ci gaba da doka wasannin gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a kasar Morocco ba saboda rauni da ta samu.

Ta samu rauni ne a wasan da Falcons ta yi rashin nasara a hannun Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu da ci 2-1 a wasan farko na rukuni na gasar.

Asisat mai shekaru 27 zata koma Barcelona wannan Alhamis, domin karin gwaje-gwaje a gwiwan nata kafin bayyana girman raunin da ta samu da kuma tsawon lokaci da zata yi jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.