Isa ga babban shafi

CAF ta sauya lokacin da za'a fara gasar kofin Afirka ta 2023

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta sauya jadawalin gasar neman cin kofin nahiyar da za’ayi a Cote d’Ivoire, inda ta dage zuwa karin watanni shiida.

Kofin gasar kwallan kafar Afirka
Kofin gasar kwallan kafar Afirka © AFP - GABRIEL BOUYS
Talla

Shugaban hukumar Patrice Motsepe ya sanar da dage gasar daga shekarar 2023 zuwa watan Jarairun 2024.

Tun farko an tsara gudanar da gasar ne tsakanin watan Yuni zuwa Yulin 2023, amma an dage saboda fargabar yanayin, don lokaci ne damuna ne da ake mamakon ruwan sama a yankin.

Da yake jawabi a Rabat na kasar Morocco, Shugaban CAF yace dole ne su dauki matakin saboda gudun kasada.

Karo na biyu

Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da ake dage gasar ta AFCON, bayan da aka dage gasar ta karshe a Kamaru, wanda inda Senegal ta samu nasarar lashe wa bayan doke Masar a bugun fanariti a wasan karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.