Isa ga babban shafi
Wasanni

Hukumar CAF ta fitar da jadawalin zagayen gasar AFCON na biyu

Hukumar ta fitar da jadawalin yadda wasannin zagaye na biyu a gasar cin kofin kasashen Nahiyar da ke gudana a Kamaru za su kaya, wasannin da za a fara daga ranar Lahadi mai zuwa.

Patrice Motsepe Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika
Patrice Motsepe Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika © AFP / Daniel Beloumou Olomo
Talla

Burkina Faso za ta kara da Gabon, sai Najeriya da Tunisia, Guinea kuma za ta fafata da Gambia, yayin da za a kece raini tsakanin Kamaru mai masaukin baki da Comoros.

Sauran wasannin na zagayen da ya kunshi kasashe 16, sun hada da karawa tsakanin Senegal da Cape Verde, sai Morocco da Malawi, Ivory Coast za ta fafata da kasar Masar, yayin da Mali za ta kece raini da Equatorial Guinea.

Patrice Motsepe Shugaban hukumar CAF da wasu daga cikin tsofin shugabanin hukumar ta CAF a baya
Patrice Motsepe Shugaban hukumar CAF da wasu daga cikin tsofin shugabanin hukumar ta CAF a baya © Photos AFP & AP - Montage RFI

A wasannin karshe na matakin rukuni da aka fafata jiya Alhamis a gasar cin kofin kasashen Afirkan a ranar Alhamis, Ivory Coast ta fitar da Algeria mai rike da kofi, bayan lallasa ta da 3-1, yayin da Equatorial Guinea ta doke Saliyo da ci 1-0.

Ita ma Mali ta lallasa Mauritania ne da 2-0, sai kuma Gambia da ta doke lallasa Tunisia da 1-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.