Isa ga babban shafi

Morocco za ta karbi bakuncin wasan karshe na gasar zakarun Afirka

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF, ta ce kasar Morocco ce za ta karbi bakuncin wasan karshe na gasar cin kofin Zakarun kungiyoyin nahiyar ta Afirka wato CAF Champions League, a ranar 30 ga watan nan na Mayu.

Kofin gasar zakarun kungiyoyin nahiyar Afirka.
Kofin gasar zakarun kungiyoyin nahiyar Afirka. AFP - MOHAMED EL-SHAHED
Talla

Sai dai CAF ba ta bayyana birnin kasar ta Morocco da za a buga wasan karshen a cikinsa ba, a tsakanin Agadir, da Marrakech, da Rabat, da Tangiers da kuma Casablanca.

Tun da fari dai kasar ta Morocco da kuma Senegal ne suka gabatar wa da hukumar CAF tayin karbar bakuncin wasan karshen na gasar kwallon kafar ta Zakarun Afirka.

Ana sa ran za a buga wasan karshen CAF Champions League ne a tsakanin kungiyar Al Ahly ta Masar da kuma Wydad Casablanca ta mai masaukin baki Morocco, kasancewar a zagayen farko na wasannin kusa da karshe da aka buga a gasar Zakarun nahiyar Afirkan, Wydad Casablanca ta lallasa Petro Luanda da kwallaye 3-1 a Angola, yayin da Al Ahly ta lallasa EntenteSetif har gida a Algeria da kwallaye 4-0.

Za kuma a buga zagaye biyu na wasannin kusa da na karshen a ranakun Juma’a da Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.