Isa ga babban shafi
Afrika

Kano Pillars da Enugu Rangers sun samu nasara a gasar zakarun Afrika

Kungiyar Enugu Rangers ta doke Vital 0 ta Burundi ci 2-0 wanda kuma ya ba kungiyar nasarar tsallakewa zuwa zagayen kusa da kwata Fainal. Wasa tsakanin Vita Club ta Congo ta Zamalek ta Masar an tashi ne babu ci amma kungiyar Zamalek ce ta tsallake bayan samun nasara ci 1-0 a karawa ta farko.

Fafatawa tsakanin Berekum Chelsea  da Zamalek
Fafatawa tsakanin Berekum Chelsea da Zamalek
Talla

A birnin Soweto kungiyar Orlando Pirate ta Afrika ta kudu ta doke Zanaco ta Zambia ci 2-1.

Sauran kungiyoyin da suka tsallake zuwa zagaye na gaba sun hada da Esperence mai rike da kofin gasar ta Tunisia da kungiyar Kano Pillars ta Najeriya da Recreativo lobilo ta Angola da kuma kungiyar stade Mallian ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.