CAF
AC Leopards ta lashe Confederation Cup
Kungiyar AC Leopards ce ta Congo Brazzaville ta lashe Confederation Cup a jiya Lahadi bayan doke kungiyar Djoliba ta Mali ci 2-1. A wasan farko da aka gudanar a Mali an ta shi wasa ne ci 2-2 wanda ya ba Leopards jimillar kwallaye ci 4-3.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan ne dai karon farko da kungiyar Congo Brazzaville ta lashe kofin hukumar CAF shekaru sama da 30 da suka gabata.
Kuma yanzu Kungiyar Leopards ta karbi kudi ne Dala 660,000 inda kuma za ta nemi lashe wasu kudin a wasan Super Cup idan ta doke Al Ahly ta Masar da ta lashe kofin Zakarun Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu