Isa ga babban shafi
Wasanni

Ghana da Najeriya za su fafata kan tikitin zuwa Qatar a Maris

Hukumar kwallon kafar Najeriya NFF, ta ce tawagar ‘yan wasan kasar ta Super Eagles za su fafata da takwarorinsu na Ghana a wasan neman tikitin. zuwa gasar cin kofin duniya da kasar Qatar za ta karbi bakunci, a filin was ana MKO Abiola da ke birnin Abuja.

Babban filin wasa na Al-Rayyan da ke kasar Qatar, wanda zai karbi bakuncin wasannin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022.
Babban filin wasa na Al-Rayyan da ke kasar Qatar, wanda zai karbi bakuncin wasannin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022. - AFP
Talla

Sanarwar ta NFF ta ce za a yi wannan karawar ce a ranar 27 ga watan Maris.

A halin yanzu ana dakon sanarwa daga hukumar kwallon kafar Ghana, kan zagayen farko na wasan neman cancantar da za su buga, wanda ake sa ran ya gudana ko dai a ranar 23 ga watan na Maris ko kuma a ranar 24 ga watan.

Baya ga wasan Najeriya da Ghana, Jadawalin wasannin neman tikitin halartar gasar cin kofin Duniya da za ta gudana a Qatar ya nuna cewa Masar da Senegal za su sake kece raini a cikin watan Maris, inda kowace kasa za ta yi tattaki zuwa gidan abokiyar hamayyarta.

A sauran wasannin neman tikitin zuwa gasar ta cin kofin duniya a Qatar, Kamaru za ta kara da Algeria, Mali da Tunisia, sai kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da za ta fafata da Morocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.