Isa ga babban shafi
Wasanni - FIFA

Gasar cin kofin Duniya duk bayan shekaru 2 alheri ne ga kwallon kafa - FIFA

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino, ya ce shirya gasar cin kofin duniya a duk bayan shekaru biyu zai haifar da fa'ida mai yawan gaske ga hukumomin kwallon kafar a matakin kasashe mambobinta.

Kofin Duniya
Kofin Duniya Jewel SAMAD AFP/Archives
Talla

Infantino ya bayyana haka ne bayan taron koli ta kafar bidiyo na masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa da FIFA ta jagoranta a ranar Litinin domin tattaunawa akan sabon shirin.

Sai dai ba a kada kuri'a akan batun ba, kuma yayin ganawa da manema labarai, shugaban hukumar ta FIFA ya ki tabbatar da ko za a kada kuri’ar akan yin gasar cin kofin duniya duk bayan shekaru 2, a lokacin taron koli na gaba da FIFA za ta yi a ranar 31 ga Maris.

To amma Infantinon ya bayyana fatan cewa ba za a yi watsi da shirin ba, wanda ya haifar da cece-kuce a duniyar kwallon kafa, sakamakon zazzafar adawar da hukumomin kwallon kafar nahiyar Turai da kuma na Kudancin Amurka ke nunawa akan shirin.

Masu ruwa da tsaki akan harkar kasuwanci dai sun kiyasta cewa, za a samar da kusan dala biliyan 4 da miliyan 400, kwatankwacin euro biliyan 3 da miliyan 9 na karin kudaden shiga cikin shekaru hudu ga hukumomin kwallon kafa idan har za a rika gudanar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekaru 2.

Zalika a kokarin shawo kan  hukumomin kwallon kafa 211 dake matsayin manbobin FIFA, hukumar ta sha alwashin mika musu karin dala miliyan 19 a duk shekara hudu ga kowannen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.