Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

United ta dare Teburin Premier, Inter ta lallasa Juventus

Manchester United ta dare saman Teburin Premier, A Seria A kuma Inter Milan ta lallasa Juventus. A Bundeliga Bayern Munich ta bude sabon babin jagorancin Tebur da maki 7. Har yanzu kuma maki 8 ne tsakanin Bercelona da Real Madrid a La liga, yayin da a Faransa kuma Marseille ta fara jayayyar Tebur da PSG.

'Yan wasan Inter Milan suna murna bayan doke Juventus ci 3-1 a Seria A
'Yan wasan Inter Milan suna murna bayan doke Juventus ci 3-1 a Seria A REUTERS/Giorgio Perottino
Talla

Ingila
A karshen mako Robin Van Persie ya taimakwa Manchester United doke tsohuwar kungiyar shi Arsenal ci 2-1 a Old Trafford.

Wannan nasarar ce kuma ta ba United damar darewa saman Teburin Prmier bayan kungiyar Chelsea ta yi kunnen doki da Swansea.

Saura kadan dai Manchester City ta cim ma United da yawan maki amma Roberto Mancini ya yi hasarar maki biyu bayan tashi wasa babu ci tsakanin City da West Ham.

Sir Alex Ferguson dai ya yaba da yadda Van Persie ya buga wasan ba tare da la’akari da tsohon baban shi ba Arsene Wenger, a haduwarsu ta farko bayan dan wasan ya yi bankwana da Emirate zuwa Aold Trafford.

Yanzu haka kuma Van Persie ya zira wa Manchester United kwallaye 10 a raga hadi da kwallon da ya zira a ragar Arsenal.

A karshen mako dai wasa ba ta yi wa Chelsea dadi ba, kamar yadda kocin The Blues Roberto Di Matteo yace wannan abun kunya ne.

Luis Suarez kuma ya taimakawa Liverpool barke kwallon da Newcastle ta zira a ragarta inda aka tashi wasan kunnen doki ci 1-1.

Italiya

A Seria kuma Inter Milan ta lallasa Juventus ci 3-1, wanda hakan ya karya lagon Juventus na buga wasanni kusan 50 ba tare da samun galabarta ba.

A wasanni 10 da Juve ta buga a bana, kwallaye 5 ne kacal aka zira a ragarta, amma Diego Milito da Rodrigo Palacio da Arturo Vidal su ne suka zira kwallaye a ragar Juventus.

Yanzu tazarar maki daya ne kacal Juventus taba Inter Milan a Teburin Seria A, kafin Napoli ta kai wa Juventus ziyara nan da makwanni biyu.

Faransa
A faransa Toulouse ta sha kashi hannun Bordeaux ci 1-0 wanda hakan ya hana kungiyar tsallakawa saman Tebur. Kungiyar Marseille ta doke Ajaccio ne ci 2-0. Kuma yanzu makinta daya da Paris Saint-Germain. Wacce ta sha kashi hannun Saint-Etienne ci 2-1.

Kungiyar Lyon dai ta lallasa Bastia ne ci 5-2.

Jamus

A Bundesliga kuma Bayer Leverkusen ita ce a matsayi na hudu a Teburin gasar bayan doke Fortuna ci 3-2. Dortmund kuma ta koma matsayi na Biyar ne bayan ta shi wasa babu ci tsakaninta da Stuttgart. tazarar Maki bakwai ne yanzu Bayern Munich ke jagorancin Bundesliga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.