Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Chelsea ta doke United, Real ta lallasa Alcoyano, Marseille ta sha kashi

A daren jiya Laraba kungiyar Chelsea ta rama kashin da ta sha a hannun Manchester a karshen mako, Bayan an tashi wasa ci 5-4 a Carling Cup. Wannan ne ya ba ‘Yan wasan The Blues damar tsallakewa zuwa Quarter Final.

'Yan wasan Chelsea suna murnar kwallon da Sturridge ya zira a ragar Manchester
'Yan wasan Chelsea suna murnar kwallon da Sturridge ya zira a ragar Manchester Reuters
Talla

Kungiyar Norwich City ta lallasa Tottenham Hotspur ci 2-1. Liverpool kuma ta sha kashi ne a hannun Swansea City 3-1.

A Copa Del Ray kuma a kasar Spain , Real Madrid ta doke Alcoyano ci 4-1, Karim Benzama da Kaka suna cikin wadanda suka zira wa Madrid kwallayenta a raga.
Mourinho dai ya ajiye manyan ‘Yan wasan shi da suka hada da Iker Casillas, Pepe, Sergio Ramos, Xabi Alonso, Mesut Ozil da kuma Cristiano Ronaldo.

A Faransa kuma kungiyar PSG ta tsallake zuwa zagayen Quarter Final bayan doke abokiyar hamayyarta Marseille ci 2-0 a gasar neman lashe kofin Faransa.

Kocin PSG Carlo Ancelotti ya buga wasa ne ba tare da manyan ‘Yan wasan shi ba da suka hada da Zlatan Ibrahomovic.

Kungiyar Nice kuma ta lallasa Lyon ci 3- 1, Kamar yadda Bordeaux ta sha kashi hannun Montpellier ci 1-0.
A Seria A a kasar Italia yanzu tazarar maki 6 Juventus taba Napoli, bayan Juve ta doke Bologna ci 2-1 a jiya Laraba.

A daya bangaren kuma Inter Milan ta smau sa’ar doke Sampdoria ci 3-2, Roma kuma tasha kashi ne hannun Perma ci 3-2.
Tun a ranar Talata ne aka tashi wasa ci 2-2 tsakanin AC Milan da Palermo.

Kungiyar Juventus ce ke jagorancin Teburin Seria A, Inter Milan ce kuma ke bi mata a matsayi na biyu sai Napoli a matsayi na uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.