Isa ga babban shafi
French League-La liga

PSG ta karyata Rahoton zawarcin Cristiano

Shugaban kungiyar PSG Nasser Al Khelaifi attajirtin kasar Qatar ya karyata rahotannin da ke cewa kungiyar shi za ta ware kudi euro Miliyan 100 domin Sayen dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo da kocin shi Jose Mourinho. Kodayake attajirin bai musanta bukatar dan wasan ba, amma yace babu wata tattaunawa tsakanin shi da shugabannin kungiyar Real Madrid kamar yadda jaridar Gazzetta Dello ta kasar Italia ta ruwaito.

Cristiano Ronaldo a lokacin da ya ke murnar zira kwallo a ragar  Manchester City
Cristiano Ronaldo a lokacin da ya ke murnar zira kwallo a ragar Manchester City
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.