Isa ga babban shafi

Bincike ya gano alaka tsakanin Le Pen da shugaba Putin

Kwamitin majalisar dokokin Faransa ya gano jam'iyyar National Rally mai ra'ayin mazan jiya ta Marine Le Pen ta yi kusanci ta kud-da kud da gwamnatin Rasha tare da saukaka yada manofofin Kremlin.

Shugaban jam'iyyar adawa a Faransa Marine Le Pen
Shugaban jam'iyyar adawa a Faransa Marine Le Pen REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Marine Le Pen da jam’iyyarta ta RN ta sha musanta zargin alaka da Vladamir Putin, to sai dai rahoton kwamitin bincike na majalisar dokoki da ‘yan jaridu suka samu tun kafin wallafa shi ya bankado fiye da abin da ake zargi tun farko.

Bayan kwashe sama da watanni shida na bincike kan korafe-korafe sama da 50, kwamitin majalisar ya gano cewa jam'iyyar National Rally (RN) wadda a da ake kira National Front, ta kasance tashar sadarwa ga gwamnatin, tare da goyon baya ga Moscow a mamayar da ta yi wa yankin Crimea.

Rahoton binciken da ake shirin wallafa a mako mai zuwa, a ranar Alhamis ya samu amincewa da kuri’u 11 kan biyar, matakin da ya fusata shugaban binciken kuma mai gabatar da kara, dan majalisar RN Jean-Philippe Tanguy, wanda ya yi watsi da tsarin da aka bi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.