Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Zan fitar da dakarun Faransa daga NATO idan na ci zabe - Le Pen

Yar takarar neman shugaban kasar Faransa a zabe zagaye na biyu Marine Le Pen ta bayyana cewa muddin ta lashe zaben kasar, to za ta aiwatar da wasu sauye-sauye dangane da siyasar kasar Faransa a kungiyar tsaro ta Nato.

'Yar takarar neman shugabancin Faransa Marine Le Pen yayin ganawa da manema labaru gabanin karawarta da Macron.12/04/22.
'Yar takarar neman shugabancin Faransa Marine Le Pen yayin ganawa da manema labaru gabanin karawarta da Macron.12/04/22. AP - Francois Mori
Talla

A ranar Laraba Marine Le Pen ta kare muradunta da manufofin jam’iyyar da take shugabanta na cewa mudin ta lashe zaben kasar, za ta nemi ganin kungiyar kasashen NATO ta kusanci Rasha wacce ta kaddamar da yaki a Ukraine.

Uwargida Le Pen ta bayyana cewa martabar Faransa da Turai ne domin babu wata nasara ko ci gaba ga Amurka na ganin Rasha da China sun kula hulda mai karfi a wannan lokaci da kasashen duniya ke dandana kudar su  biyo bayan barkewar wannan yaki tsakanin Ukraine da Rasha.

Janyewa daga NATO

Kazalika yar takarar jam'iyyar RN ta jaddada cewa mudin ta lashe zaben zagaye na biyu da zai gudana nan da kwanaki 11, Faransa za ta janye dakatun ta daga cikin kungiyar tsaro ta Nato, kungiyar da ta shiga a shekara ta 2009 a karkashin shugabancinNicolas Sarkozy.

Kare muradun Rasha

Yayinda yar takarar ke kokarin samun goyan da ya dace daga Faransawa, abokin hamayar ta  kuma shugaban kasar Emmanuel Macron ya danganta Marine Le Pen amatsayin mai kokarin kare muradun Rasha da kuma neman mayar da hannun agogo baya, ganin jan kokarin da gwamnatin sa ta yi tsawon Shekaru.

Yayinda yan takaran kowanen su ke yakin neman zabe, hasashe na nuni cewa Shugaba Emmanuel Macron na kan hanyar lashe wannan zabe da sama da kashe 45.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.