Isa ga babban shafi

Macron da Le Pen sun yi wa abokan takararsu fintinkau a zaben Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai fafata da Marine Le Pen a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a yi nan gaba saboda gazawa wajen samun isassun kuri’un da zasu bashi nasara kai tsaye.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da jagorar 'yan adawa Marine Le Pen.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da jagorar 'yan adawa Marine Le Pen. AFP - ERIC FEFERBERG,ALAIN JOCARD
Talla

Kafar talabijin din kasar tace sakamakon farko ya nuna cewar Macron ya samu kashi 28.1, yayin da Le Pen ta zo ta biyu da kashi 23.3.

Jean-Luc Melencheon ya zo na 3 da kusan kashi 20 daga ‘Yan takara 12 da suka fafata a zaben na yau.

Shugaba Macron na neman ganin ya zama shugan Faransa na farko da ya samu wa’adi na biyu a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Hukumomin kasar sun ce kashi 65 na masu kada kuri’u ne suka fito domin yanke hukunci akan wanda suke so ya zama shuagban kasa.

Eric Zemmour wanda yayi kaurin suna wajen zazzafar ra’ayin say a samu kasha 7.2 na kuri’un da aka kada, yayin da Valerie Pecresse daga Jam’iyyar konzabatib ta samu kasha 5 na kuri’un da aka kada wanda shine mafi muni a tarihin Jam’iyyar.

Tuni wasu daga cikin Yan takaran zaben shugaban kasar suka bayyana goyan bayan su ga shugaba Macron wajen ganin ya kayar da Le Pen a zagaye na biyu na karawar da za’ayi.

Daga cikin su akwai Fabien Roussel da Anne Hidalgo da Yannick Jadot da kuma Valerie Pecresses.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.