Isa ga babban shafi
Faransa-Zabe

'Yan siyasar Faransa na fuskantar barazana daga tsageru gabanin zaben kasar

‘Yan siyasar Faransa sun bayyana fargaba kan yadda rikice-rikice masu alaka da zabe ke ta’azzara dai dai lokacin da babban zaben kasar na watan Aprilu ke karatowa.

Zaben na bana zai fi daukar hankali fiye da wadanda suka gabace shi saboda yadda za a gwabza tsakanin shugaban mai ci da masu tsattsauran ra'ayi.
Zaben na bana zai fi daukar hankali fiye da wadanda suka gabace shi saboda yadda za a gwabza tsakanin shugaban mai ci da masu tsattsauran ra'ayi. AFP - JACQUES DEMARTHON
Talla

Jam’iyyar mai mulkin Faransa ta Republican on the Move na cikin ‘yan gaba gaba da suka mika korafin yadda tashe-tashen hankula masu alaka da zaben kasar ke tsananta, bayan gobarar gidan dan Majalisa Pascal Bois wadda ta kone dakin adana motocinsa kwanaki kalilan bayan kirsimati.

Bois wanda ko cikin watan Nuwamba ya samu wani sakon wasika dauke da harsashi da ke yi masa gargadi kan sake tsayawa a zaben kasar, ya ce tashin gobarar ya matukar firgita shi tare da iyalinsa baki daya.

Gobarar gidan dan majlisar ta zo ne a dai dai lokacin da Majalisa ke tafka muhawara kan dokar tilasta karbar allurar rigakafi a kasar, dokar da mambobin jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron ke goyon baya.

Wasu alkaluma da hukumar ‘yan sandan Faransar ta tattara ya sanar da karuwar barazana ga ‘yan siyasa watanni 3 gabanin zaben shugaban da kuma zaben ‘yan majalisu na watan Yuni.    

Alkaluman da hukumar ta tattara ya ce cikin watanni 11 na farkon 2021 ‘yan siyasa dubu 1 da 186 sun shigar da korafe-korafen kai musu farmaki ko kuma aike musu da sakon barazana ciki har da ‘yan majalisa 162 da yanzu haka ke bakin aiki, adadin da ya kara yawan makamantan korafe-korafen da ake samu da akalla kashi 47.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.