Isa ga babban shafi
Faransa-Zaben Faransa

'Yan takara 12 za su fafata da juna a zaben Faransa

Kotun Fasalta Kundin Tsarin Mulkin Faransa ta amince da ’yan takara 12 da za su fafata a zagayen farko na zaben shugabancin kasar da zai gudana a watan Afrilu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na cikin masu fafatawa a zaben shugabancin kasar
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na cikin masu fafatawa a zaben shugabancin kasar REUTERS - POOL
Talla

Shugaban Kotun Laurent Fabius ya bayyana sunayen ‘yan takarar 12 cikin wata sanarwa da aka watsa ta bidiyo da sanyin safiyar wannan Litinin.

'Yan takarar 12, waɗanda suka sami sa hannun magoya baya 500 daga aƙalla kananan hukumomi 30 kamar yadda dokokin zabe suka tanadar akwai Marine Le Pen na jam’iyyar (RN) masu tsatsauran ra’ayi da Eric Zemmour (Reconquest!) mai tsanin kyamar baki da Nicolas Dupont-Aignan na jam’iyyar (DLF),  sai Valérie Pécresse (LR). ),

Sauran ‘yan takara da kotun ta amince da takarar su a zagen farko na zaben shugaban kasa na ranar 10 zuwa 24 ga watan Afrelu sun hada da shugaba mai ci Emmanuel Macron na jam’iyyar (LREM) da Anne Hidalgo magajiyar birnin Paris daga jam’iyyar (PS), sai Yannick Jado (Ecologiste) mai rajin kare muhalli sai Jean-Luc Mélenchon (LFI).. da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.