Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Faransawa sun kada kuri'a a zagayen farko na zaben shugaban kasa

Wannan Lahadi 10 ga watan Afrilun shekarar 2022, Faransawa suka kada kuri'a a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka yi hasashen sai an kai ga zagaye na biyu tsakanin shugaba mai ci tsakanin Emmanuel Macron da bababar abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen mai tsatsauran ra'ayi wanda zai yi tsauri fiye da fafatawar da suka yi shekaru biyar da suka gabata.

Wani ma'aikaci ne dauke da akwatin zabe yayin da yake wucewa a gaban wata rumfar zabe mai launin tutar Faransa, blue, fari da ja, a lokacin shirye-shiryen da ake yi a wurin zaben shugaban kasar da za a gudanar a Le Touquet-Paris-Plage, Faransa 6 ga Afrilu. , 2022.
Wani ma'aikaci ne dauke da akwatin zabe yayin da yake wucewa a gaban wata rumfar zabe mai launin tutar Faransa, blue, fari da ja, a lokacin shirye-shiryen da ake yi a wurin zaben shugaban kasar da za a gudanar a Le Touquet-Paris-Plage, Faransa 6 ga Afrilu. , 2022. REUTERS - PASCAL ROSSIGNOL
Talla

Da misalin karfe 0600 agogon GMT ne aka bude rumfunan zabe a wasu sassan Faransa, bayan wani yakin neman zabe da ba sabon ba, sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, wanda manazarta suka yi gargadin ka iya bada mamaki a zaben na Faransa, da kuma watakila a fuskanci rashin fitowar jama’a.

Wasu sun kada kuri'u ranar Asabar

Tuni wasu Yankunan Faransa na ketare suka riga suka kada kuri'unsu a ranar Asabar saboda bambancin lokaci, masamman karamin tsibiri na Saint Pierre da Miquelon da ke gabar tekun Kanada sannan kuma yankuna dake Caribbean sai tsibiran Fasifik na Faransa.

Zagaye na biyu

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta yi hasashen cewa Macron zai jagoranci Le Pen da 'yan kadan na maki a zagaye na daya, yayin da manyan biyu za su kai ga zagaye na biyu a zaben da za a yi ranar 24 ga watan Afrilu.

Dan takarar jam’iyyar hagu Jean-Luc Melenchon yana kan gaba a matsayi na uku kuma har yanzu yana sha'awar damar zuwa zagaye na biyu a kan Le Pen ko ma ya bada mamaki zuwa na daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.