Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Zaben Faransa: Tarihin Melanchon dan takarar shugaban kasa

An haifi Jean Luc Melenchon ne a 1951 a garin Tanger na Morocco, ya yi karatunsa ne a fannin falsafa da nahawun zamani. Dan gurguzu ne a 1986 ya zama sanatan faransa  mafi kankantar shekaru.

Jean-Luc Melenchon
Jean-Luc Melenchon REUTERS - Pascal Rossignol
Talla

A tsakanin 2000 da 2002 ya rike mukamin ministan koyar da ayukan fasah.  Har ila yau bayan shekaru 20 ya sake zama ministan da ya fi maida hankali sosai a wajen da dama daga cikin ma’aikatan ministan ilimi.

Ya shugabanci bangaren masu tsarin ra’ayi na jam’iyar gurguzu ta PS, inda ya yi kokowar nuna adawa da bin sahun yan social-démocratie na turai.

Bayan nasarar da bagaren masu sassaucin ra’ayi na yan gurguzu ya fice daga jam’iyar ta Socialiste PS 2008 inda ya kafa tasa jam’iyar bagaren hagu Front de Gauche. A karkashinta ya zama dan majalisar dokoki 2009, an sake zabensa a 2014.

Ya yi takarar kujerar shugabancin kasar Faransa a zaben 2012, inda a zagayen farkya samu yawan kuri’un miliyan 4 (11,1 %).

A watan fabrairun  2016, ya sake gabatar da takarasa a zaben shugabancin kasar 2017  inda a zagayen  ya hada kan kuriu miliyan 7 20%.  Ya zama dan majalisar dokoki dake wakiltar yankin  Bouches-du-Rhône, à Marseille, da kimanin  60% na kuriun da aka kada

Marubuci ne da ya rubuta litattafa 19  daga ciki a kwai  « l’Ere du peuple », wanda ya sayar da duban kofi inda yake ilimatar da yadda al ‘umma ya kamata ta bijire

Jean-Luc Mélenchon ya samu babbar lambar karamawa ta kasar Argentina.

Yanzu kuma ya sake gabatar da takararsa a zaben shugabancin kasa na 2022 da za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Avrilu  a karkashin tarayyar al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.