Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Zaben Faransa: An kawo karshen yakin neman shugaban kasa

Yau Juma’a 8 ga watan Afrilun shekarar 2022 ake kawo karshen yakin neman zaben shugabancin kasar Faransa, wanda ‘yan takara goma sha biyu ke fafatawa ciki har da shugaban kasar Eammanuel Macron.

Hotunan 'yan takarar shugaban kasa a birnin Mouguerre da ke kudu maso yammacin Faransa, Litinin 28 ga Maris, 2022.
Hotunan 'yan takarar shugaban kasa a birnin Mouguerre da ke kudu maso yammacin Faransa, Litinin 28 ga Maris, 2022. AP - Bob Edme
Talla

Masu kada kuri'a za su fito a zagayen farko na zaben shugaban kasar Faransa a ranar Lahadi, inda shugaba Emmanuel Macron ke neman wa'adi na biyu na shekaru biyar.

'Yan takara biyu na farko a zagayen farko ne za su ci gaba zuwa zagaye na biyu na zaben, wanda za a yi a ranar 24 ga watan Afrilu. Ana sa ran Macron zai kasance daya daga cikin wadanda za su yi gaba da gaba, sai dai har yanzu akwai yuwuwar kammala zaben ranar Lahadi ya zama abin mamaki.

Emmanuel Macron

Shugaban mai shekaru 44 da haifuwa a cikin 'yan makonnin nan ya mayar da hankali ne kan harkokin diflomasiyya, inda masu sharhi suka ce yakin da Rasha ta yi a Ukraine ya taimaka wajen bunkasa martabarsa.

Le Pen

Wadda ake gani a matsayin babbar abokiyar hamayyara shaugaba Macron dai ita ace Mariane Le Pen, wadda ta kasance ‘yar atakara mai ra’ayin rikau, kuma wannan shaine karo na uku da take tsayawa takarar shuagabancin kasar, abin da masana ke kallon matsawara ta gaza samun nasara hakan ka iya kawoa karshena salon tata siyasar.

Melenchon

Jean-Luc Melenchon mai ra'ayin rikau daga jam'iyyar Rassemblement National wadda a da ta kasance National Front shi ne ke biyewa Le Pen, da kashi 21.9 cikin dari.

Zemmour

Eric Zemmour wanda tsohon dan jarida ne, shiama na fadi tashin yadda zai hau ragamar akasar saia dai sakamakon kyamar addinin Islama da bakin haure, da farko ya yi nasarar janyo hankalin ‘yan jari hujja

To sai dai kuma a kuri'ar jin ra'yoyin jama'a da aka gudanar a baya-bayan nan, ya yi kasa sosai saboda salon sa na rashin sassauci, inda ya koma matsayi na hudu da kashi 10 cikin 100.

Pecresse

Valerie Pecresse ‘yar takarar jam'iyyar ‘yan gurguzu, bayan nasarar zaben fidda gwani, wanda ya kasance gidan siyasa ga tsoffin shugabannin kasar Nicolas Sarkozy da Jacques Chirac, Pecresse ta zama 'yar takara mace ta farko da jam'iyyar ta sayar, sai dai kuma ana ganin akwai tarin kalubale da ke gabanta wajen yanyo kan hankalin al’ummara kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.